Kalaman Soyayya Masu Dadi

Kalaman Soyayya Masu Dadi


















Ina son ganinki a gefena, rashinki babban ciwo ne a zuciyata. Babu second din da yake wucewa ba tare da tunaninki a kwakwalwata ba, Ina kewarki my love.



 Babu abinda ya kai rashinka zafi da kuna a zuciyata, please ka dawo kusa dani, ba zan iya cigaba da jurar rashinka a tare da ni ba masoyi Ina kewarka.


Kadaicin rashinki ya addabi zuciyata, idanuna da kunnuwana suna maraicinki, rayuwa babu ke tamkar rayuwa ba wani baren jikina ne.

 Baby Ina kewarka irin sosai din nan, ko da yaushe burin zuciyata ta gammu a tare da kai shiyasa a duk lokacin da kayi nisa da ni nake azabtuwa da kewarka.

 Na kasa daina tunaninki, kuma a duk lokacin da na tunaki, zuciyata tana kuka saboda rashinki, Nayi matukar kewarki hubbyna.
Al - ameen Kai ne madarar zuciyata, inda zan sama dama daya da na fasa kirjina na zaro zuciyata na mika ta gare ka , ta zama itace tukwici ga jin sautin muryarka da kan jefa zuciyata murna da nishadi a duk sa'ada kayi magana . Nayi alkwarin kasancewa a tare da kai cikin zafi ko sanyi tsanani ko dadi .

Fadeelah kyawanki ne yasa har yau na gaza yarda da cewa yan matan larabawa ko indiyawa kyawawane, domin duk sanda na kalli yar india kuma na kalle ki sai inga ta zamto tamkar bakin gawayi a gaban farin wata . Kina da kyawan sura ke tamkar zinariya ce a cikin yan mata . Na dade da zama naki, ki ceci rayuwata ta hanyar zamowa tawa , in ba haka ba zan zamto tamkar gangar jikin da ba lumfashi a tare da shi.

Habib Soyayyarka a zuciyata kullum takan kyankyashi kwayaye marar adadi yanzu haka ta war - watsu a ciki birni da kauyukan zuciyata ta ratsa jini da jijiya ta shiga bargo da hanta shin me kake tunanin zai iya rabani da soyayyarka ? Karkayi yunkurin rabuwa da ni . domin hakan dai dai yake da yunkurin raba ni da rayuwata

Fatima Soyayyarki tamkar bishiyace da ta kafu a karkashin zuciyata ta saki rassai da jijiyoyi cireta ba abu mai yuyuwa bane . Bazan rayuwa ba idan bakya raye zan kuma iya mutuwa domin ki rayu.

Tirsasawa zuciyar ka son wanda ya nuna yana son ka a zahiri babbane ko yaro , talakane ko mai kudi , mace ko namiji , kyakkyawa ko akasin hakā .

Sonki ya narkar da zuciyata, mutane sukan kirani zautacce marar zuciya a kan sonki, kwarai na zabi su kirani da mahaukaci a kan sonki, domin malaman tarihi masana soyayya sun tabbatar da cewa so ba zai taba cika so ba sai an hada da hauka, yanzu ne na tabbatarwa da kaina ni cikakken masoyine tunda ina haukan sonki.

Sau da dama nakanji tamkar in kai kaina asibiti a farka kirjina a ciro zuciyata a gabanki domin a nuna miki irin yawan so da kaunarki dake cikinta, sai dai kash nasan hakan ba abu ne mai yuyuwa ba. Amma na sadaukar da komai nawa gareki ki yarda ni sadauki ne a cikin masoyanki.

 Idan bakya kusa dani, duk wani abu mai kyau a duniya muninsa nake gani, rashinki ya cutar da zuciyata Ina kewarki masoyiya.

 Kewarka ta zama wani bangare na jikina, kamar bacci da lumfashi, duk inda na kalla sai in ganka kana yi min gizo a idanuna. Ina sonka.